X

Dangote ya rage farashin man dizal zuwa Naira 1,000 / lita

Matatar man Dangote ta dala biliyan 20 ta rage farashin man dizal da kashi 16.6 zuwa Naira 1,000 a kowace lita, daga Naira 1,200 kan kowace lita domin taimakawa wajen yin tasiri ga tattalin arzikin cikin gida na Najeriya.

Farashin man dizal ya yi tsada na tsawon watanni,sakamakon shigo da kayayyakin daga kasuwannin duniya da kuma matsalar canjin kudaden waje da ke da nasaba da shi.

Sai dai a wata sanarwa da Vanguard ta samu a yau, kamfanin ya bayyana cewa: “A wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba, matatar man Dangote ta sanar da kara rage farashin man dizal daga naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita.

“A yayin da ake fitar da kayayyakin, matatar ta samar da ita a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 a kowace lita makonni uku da suka gabata, wanda ya nuna sama da kashi 30 cikin 100 na raguwar farashin kasuwa a baya na kusan N1,600 kowace lita.

A cewar kamfanin, “wannan gagarumin raguwar farashin man dizal, a matatar man Dangote, ana sa ran zai yi tasiri sosai a dukkan bangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a kasar nan.”

Kwanan nan, Shugaban Rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa karfin matatarsa na sayar da dizal akan farashi mai rahusa zai kawo sauki cikin gaggawa ga kalubalen hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Dangote ya bayyana cewa matatar man dizal na sayar da man dizal akan naira 1,200 akan kowacce lita, idan aka kwatanta da farashin kasuwa a baya na N1,650 – N1,700.

Ya kara da cewa yana sa ran raguwar farashin man fetur da zai taimaka wajen dakile hauhawar farashin kayayyaki a watanni masu zuwa.

Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar da shugaban kasa Bola Tinubu ya kai masa domin bikin Sallar Eid-El-Fitr a Legas.

Categories: Labarai
Umar Muhammad:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings