X

Dan sanda ya yi kokarin lalata da ni har da yunkurin Taba min nono – Jaruma Didi

-Wata jarumar fina-finan Nollywood, Didi Ekanem, ta bayyana yadda wasu ‘yan sanda suka ci zarafinta a Legas – A cewar jarumar, har daya daga cikinsu yana yunkurin taba ma ta nono, sannan shugabansu ya bijiro mata da bukatarsa – Tuni aka damke ‘yan sandan, bayan gano har cin hancin N100,000 suka amsa daga hannunta kafin su sakar mata motarta Wata jarumar fina-finan Nollywood, Didi Ekanem, ta ce kwanan nan wasu ‘yan sanda a jihar Legas suka ci mata zarafi. Kamar yadda jaridar Punch ta fitar da labarin ranar Lahadi, kusan ‘yan sanda 10 ne suka ci mata zarafi saboda ta saba dokar titi. A cewarta, al’amarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Nuwamba, wuraren Lekki a jihar Legas.

“Dan sanda ya yi kokarin lalata da ni har da yunkurin latsa min nono – Jaruma Didi.

“Tabbas na saba dokar titi, amma ban yi hakan da gangan ba. Na juya ne inda bai dace in juya ba, saboda ina kokarin komawa gida in sha maganin ulcer dina,” kamar yadda jarumar tace, kuma jaridar ta wallafa.

“Kafin in karasa juyawa, sai ga wasu ‘yan sanda rike da manyan bindigogi suna tunkaro motata, ni kuma na fara yi musu bayani amma ko saurara ta ba su yi ba. “Saboda sun ga ina da kananun shekaru, har nishadi suka yi ta kwasa, suna cutar dani. Take a nan na fara kuka ina fadi musu cewa nasan na karya doka. Ina rokon gafararsu, amma ko a jikinsu, suka cigaba da saita ni da bindiga.” Ekanem ta ce taki sanar musu da cewa ita jarumar fim ce, sai tace dinki da ado ne sana’arta. A cewarta, ta samu damar daukar bidiyon ‘yan sandan, wanda duk fuskokinsu suka fito. “Su kusan 10 ne, daya har yunkurin taba nonuwa na yayi, yana kokarin kwantar min da hankali. “Bayan shugabansu ya zo, sai suka ja ni har Alausa cikin Ikeja. Da ina rokonsa, sai ya fara nunamin kwadayin surata. Har yana cewa yana sona, sannan duwawuna ya ba shi sha’awa, hakan yayi matukar batamin rai.

“Daga baya sun bukaci in biya su N200,000, amma N100,000 na iya biyansu, sannan su ka bani mota ta. Tun wurin karfe 9 na safe, har wurin 6 na yamma,” cewar jarumar. A wani labari na daban, w’yan sanda da ‘yan sa kai da ke Ogwashi-Uku, karamar hukumar Aniocha ta kudu da ke jihar Delta, sun kama wasu samari 2 da akwatin gawa, cike da ‘yan kamfan mata da rigunan nono. An kama wadanda ake zargin a wuraren Agidiehe quarters da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, kamar yadda labarai suka bayyana. Sai da ‘yan sa kai suka kama su tukunna aka sanar da ‘yan sanda.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings