Sadiq Gaya, lauyan hukumar kula da kadarorin Najeriya (AMCON) ya rasu ne a ranar Talata da yamma kuma aka binne shi a Abuja.
Marigayin wanda ya kammala karatun shari’a a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma ya kammala karatunsa na digiri a jami’ar LL.M da ke Wales a kasar Birtaniya, ya bar mata daya da ‘ya’ya biyu.
A wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, Gantuve ya bayyana marigayin a matsayin mai tarbiyya, adali kuma mutuniyar al’umma.
Ya ce: “Duk da cewa mun so shi, amma Allah ya fi son nasa. Namu shi ne mu yi masa addu’a ya samu gafarar Allah da Aljannah”.
“A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, muna mika ta’aziyyarmu ga mai girma Sanata Kabiru Ibrahim Gaya da daukacin iyalansa bisa wannan babban rashi da aka yi.
“Allah Subhanahu Wata’ala Ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma saka masa da kyawawan ayyukansa. Mun samu labarin rasuwarsa cikin kaduwa.”
Sanarwar ta kara da cewa gwamnan yana gidan Sanata Gaya da ke Abuja inda ya jajanta masa da iyalansa.