An ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a hedikwatar ‘yan sandan jihar Adamawa da ke Jimeta a karamar hukumar Yola ta Arewa da sanyin safiyar Laraba, lamarin da ya jefa mazauna garin na Yola cikin firgici.
Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce an shawo kan lamarin.
Nguroje ya ce, “An dakile harin, amma ba a san ko su waye suka kai harin ba.”
Jaridar ta ruwaito wata majiya tana zargin cewa maharan jami’an soji ne da ke aikin ramuwar gayya, biyo bayan kashe wani jami’in soji.
Ko da yake jaridar ta ce ba za ta iya tabbatar da kanta ko akwai jami’an soji ba, amma ‘yan sandan sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin harin da kuma wadanda suka kai shi.