Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Zamfara ta kori karar da jam’iyyar APC ta shigar, ta kuma tabbatar da nasarar Dauda Lawan, a matsayin halastaccen zababban Gwamnan jihar Zamfara.
Idan za’a iya tunawa bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana Dauda Lawan na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar, hakan tasa Bello Muhammad Matawalle na jam’iyyar APC ya shigar da kara Inda yake ƙalubalantar nasarar da Dauda Lawan ya samu a gaban kotu.