Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd), ya bayyana sunayen kungiyon da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya sauran kasashen Sahel.
A cewarsa, Jama’at Nasr al-Islam Wal Muslimin (JNIM), Islamic and Muslim Support Group (GSIM) da ISGS sune kunyoyin da ke karfafa ayyukan ta’addanci, The Nation ta ruwaito.
UGC Hukumar ta NSA ta bukaci masu wa’azin addinin Islama da Limamai da su dauki matsaya mai kyau don tallafawa ayyukan gwamnati a yaki da ta’addanci. Ya lura cewa kawance tsakanin malamai da jami’an tsaro “ya zama kashin bayan sake gina al’ummominmu da ta’addanci suka mamaye”. Karin bayani na nan tafe…
Daga Jaridar #Legit