‘Yan fashin daji kan kwashi dalibai bila adadin su kutsa da su cikin daji daga baya su nemi kudin fansa kafin su sake su.
Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Kwara ta kafa wata rundunar mata zalla don kare makarantu daga hare-hare.
Kwamandan hukumar ta NSCDC a jihar ta Kwara, Mr Makinde Ayinla, ya ce kafa wannan runduna zai taimaka wajen kare dalibai daga masu garkuwa da mutane.
“A wannan wata na Janairu za mu kaddamar da wannan runduna ta mata don magance matsalar garkuwa da dalibai.” Mr Ayinla ya fadawa manema labarai a Ilorin babban birnin jihar ta Kwara.
A cewarsa, an riga an horar da wasu daga cikinsu, saboda haka tare da iznin gwamna, za a tura su zuwa makarantu a wannan wata, kamar yadda Channels ta ruwaito.
Matsalar satar dalibai a makarantu a arewacin Najeriya ta zama ruwan dare, ko da yake, hukumomin sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen shawo kan matsalar.
‘Yan fashin daji kan kwashi dalibai bila adadin su kutsa da su cikin daji daga baya su nemi kudin fansa kafin su sake su.
Lamarin kan rutsa har da kananan yara da ba su mallaki hankalin kansu ba.
A mafi aksarin lokuta sai an biya kudaden fansa ‘yan bindigar ke sako daliban.