Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya kori Darakta-Janar na hukumar yi wa kasa hidima ta kasa, Birgediya Janar Mohammed Fadah.
Da aka tuntubi mai magana da yawun hukumar NYSC, Eddy Megwa, kawai ya bukaci wakilinmu da ya jira wata sanarwa a hukumance da za a fitar a yau Juma’a.
Sai dai jaridar The Cable, ta nakalto majiyoyin na cewa shugaban ya dauki matakin ne a ranar Alhamis.
Korar Fadah na zuwa ne watanni shida kacal bayan nada shi shugaban NYSC a watan Mayu, 2022.