X

Bakin haure 41 ne suka mutu a kifewar jirgin ruwa a Italiya

Wasu bakin haure 41 ne suka mutu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa a tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, kamar yadda wasu da suka tsira suka shaidawa kafar yada labaran kasar.

Wasu gungun mutane hudu da suka tsira daga bala’in sun shaida wa masu aikin ceto cewa suna cikin wani jirgin ruwa da ya taso daga Sfax na kasar Tunisiya ya nutse a kan hanyarsa ta zuwa Italiya.

Mutanen hudu da suka tsira da ransu, ‘yan asalin Ivory Coast da Guinea, sun isa Lampedusa a ranar Laraba.

Fiye da mutane 1,800 ne suka rasa rayukansu a bana a hanyar tsallakawa daga arewacin Afirka zuwa Turai.

Wadanda suka tsira – maza uku da mace daya – sun shaida wa masu ceto cewa suna cikin jirgin ruwa dauke da mutane 45, ciki har da yara uku.

Sun ce kwale-kwalen nasu ya bar Sfax ne a ranar Alhamis din makon jiya, amma ya nutse cikin sa’o’i.

Sun kara da cewa wani jirgin ruwan dakon kaya ne ya kubutar da su, sannan aka tura su zuwa wani jirgin ruwa masu gadin gabar ruwan Italiya.

Jami’an tsaron gabar tekun Italiya sun bayar da rahoton cewa wasu jiragen ruwa biyu sun nutse a yankin a ranar Lahadin da ta gabata, amma babu tabbas ko wannan jirgin na daya daga cikin wadannan.

Hukumomin Tunisia sun ce Sfax, wani tashar tashar jiragen ruwa mai nisan mil 80 (kilomita 130) daga Lampedusa, sanannen kofa ce ga bakin haure da ke neman tsira da rayuwa mai inganci a Turai.

A cikin ‘yan kwanakin nan, jiragen ruwa masu sintiri na Italiya da kungiyoyin agaji sun ceto wasu mutane 2,000 da suka isa Lampedusa.

Tun a ‘yan watannin nan dai ana fama da matsalar wariyar launin fata ga bakaken fata ‘yan Afirka da kuma yunkurin ficewa daga kasar ta jirgin ruwa ya karu.

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings