Babban editan Hausa na BBC, Aliyu Tanko, wanda ya dade yana rike da wannan mukami, ya yi murabus daga aiki bayan zarge-zargen cin zarafi da tsohuwar ma’aikaciyar gidan rediyon, Halima Umar Saleh, ta yi masa.
Jaridar Independent Mirror ta ruwaito cewa, Mista Tanko ya bayyana ya yi murabus ne da kansa bayan ya yi wa BBC hidima na tsawon shekaru 17 cikin kwarewa.
Ya ki yin karin bayani kan zarge-zargen “cin zarafi” da tsohuwar ma’aikaciyar ta yi masa lokacin da take karkashinsa.
Halima Umar Saleh, wacce yanzu ita ce Babban Editan Dijital a TRT Africa, ta yi nuni a wani tattaunawa da Arewa24 cewa Mista Tanko ya ci zarafinta a lokacin da take aiki a karkashin BBC. Wannan hirar ta janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta bayan Arewa24 ta goge bidiyon daga shafinta, abin da ya haifar da zargin tsoma bakin editoci.
Wata majiya ta bayyana cewa an tura korafe-korafe da dama na ciki da waje zuwa hedkwatar BBC a Landan, inda aka nemi gudanar da bincike kan lamarin.
An tattaro cewa shugaban BBC West Africa, Ehizojie Okharedia, ya kira gaggawar taro a ranar Laraba, wanda daga bisani Mista Tanko ya bar ofis din ba zato ba tsammani.
A matsayinsa na shugaban BBC Hausa, Mista Tanko ya jagoranci tawagar ‘yan jarida da manyan ‘yan jarida a Landan da Abuja, tare da manema labarai a filin daga Najeriya, Nijar, Ghana da Kamaru.
Ya kasance mai kula da fitowar shirye-shiryen gidan rediyon Hausa, wato: watsa shirye-shirye hudu na kowace rana ta rediyo, sa’o’i 20 na dijital (shafukan yanar gizo da sada zumunta), da kuma rahoton talabijin na mako.
A karkashinsa aka kirkiri shirye-shirye kamar su Daga Bakin Mai Ita, Ku San Malamanku, Zamantakewa, Mahangar Zamani, Lafiya Zinariya, Korona Ina Mafita da sauran shirye-shiryen dijital.
Tare da tawagar ma’aikata sama da 40, sashen Hausa shi ne mafi girma a cikin dukkanin harsunan BBC a Afirka, da masu sauraro na rediyo sama da miliyan 23 a kowane mako, da kuma kusan ziyara miliyan 10 a shafin yanar gizo na mako.