Faransa ta ce “babu yanayi mai kyau” da za ta iya ci gaba da yaƙar ‘yan bindiga masu iƙirarin jihadi a Mali.
Shugaba Emmanuel Macron ya nemi a sake fasalin dakarun Faransar a yankin na Sahel.
Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce ƙasar za ta ci gaba da yaƙar ‘yan bindigar a ƙasashe maƙota.
Tuni Faransa ta rage yawan dakarunta a Mali.
A shekarar 2020 ne sojoji suka ƙwace mulki a Mali sannan kuma an yi ta samun rikici tsakanin gwamnatin da ƙasashen waje.
A watan Disamba, ƙasashe 16 – mafi yawansu a Turai – sun yi watsi da matakin gwamnatin Mali na yin aiki da sojojin haya na ƙungiyar Wagner ta ƙasar Rasha.