Autumn Spikes ta maida martani bayan Aliko Dangote ya kai ta kara a kotu – Spikes ta ce Attajirin ya yi mata tayin kudi da nufin ta rufe maganar alakarsu – Wannan mata ta ce ba ta karbi cin hancin miliyoyin da Dangote ya yi mata ba Autumn Spikes, tsohuwar buduwar Aliko Dangote, ta yi magana game da alakarta da fitaccen mai kudin Afrika wanda yanzu ya maka ta a gaban kotu. Miss Autumn Spikes ta bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi mata tayin $15, 000 a matsayin cin hanci domin ta rufe maganar alakar da ke tsakaninsu. Kamar yadda Premium Times ta rahoto, wadannan makudan kudi sun kusa kai Naira miliyan shida. Bayan haka, Autumn Spikes ta bayyana cewa babban ‘dan kasuwan ya yi mata alkawarin zai rika biyanta $2,500 duk wata idan ta yi shiru da maganar.
Wannan mata ba ta bayyana ko zuwa tsawon yaushe Dangote ya yi alkawarin zai rika ba ta $2500 ba, amma ta ce ta tanadi Lauyoyi a kan wannan lamarin. Spikes ta fallasa wannan ne a shafin ta na Instagram @allounda1 a ranar Litinin, 25 ga watan Junairu, 2021. Wannan Baiwar Allah ta fito ta na bukatar a biya ta kudi har fam Dala miliyan 5 (N1, 900, 000, 000.00) daga hannun Dangote na yarjejeniya da su kayi. Spikes ta ce ta yi watsi da tayin da ta kira na cin mutunci da Dangote ya yi mata, ta dauki hayar Lauya Paul Petruzzi ya kare ta a karar da aka kai ta a kotu.
cewar budurwar, Aliko Dangote ya tursasa mata ne ta sa hannu a yarjejeniyar NDA ba da son ranta ba, tun da mai kudin ya je kotu, ta nemi a biya ta tara. Dazu kun ji cewa fitaccen mai arzikin Najeriya, Aliko Dangote ya maka tsohuwar budurwarsa, Autumn Spikes, wanda su kayi shekaru tare a gaban kotu. Dangote ya zargi Spikes da kokarin tatsar kudi har fam dala miliyan biyar daga hannunsa. A karar da ya shigar a gaban wata kotun Amurka, lauyoyin Attajirin sun nemi a biya shi $30,000 a dalilin karya alkawari da kuma bata masa suna da aka yi.