X

Attahiru Jega ya gargadi ‘yan Najeriya kan sake zaɓen APC da PDP

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓen Najeriya, Farfesa Attahiru Muhammad Jega, ya yi kira ga ‘yan ƙasar su dawo daga rakiyar manyan jam’iyyu na APC da PDP, saboda yadda suka kasa taɓuka wani abun arziƙi a tsawon shekara 20 da suka shafe suna mulki.

Yayin wata hira ta musamman da BBC Hausa, Jega ya ce muguwar rawar da jam’iyyun biyu suka taka a tsawon waɗannan shekaru ta nuna ƙarara cewa babu buƙatar a sake yin amanna da su a kan cewa za ta sauya zani idan aka sake ba su wata dama a nan gaba.

Ya ce: “APC da PDP sun yi [mulki] duk mun gani, ba gyara suke nufi ba. 

“Idan ka dubi yaƙi da cin hanci da rashawar nan, duk mutanen da ake cewa ɓarayi ne za a hukunta su saboda sun yi sata a karkashin PDP, yanzu sun lallaba sun koma APC, kuma shiru kake ji.

Jega ya ce ”shi ya sa mu muke ganin cewa yanzu lokaci ya yi da za a samar da wata dirka da duk mutumin kirki zai koma cikinta, domin bayar da tasa gudunmawar wajen kawo gyara a Najeriya.

“Don haka ne ni tuni na yi rijista da PRP na zama dan jam’iyya don duba ta yadda zan taimaka wa Najeriya”, in ji shi.

“A halin da ake ciki ka da mutum ya ce don yana malamin makaranta shi kenan a zauna a sa ido, a bar maɓarnata a cikin jama’a su mamaye iko.

“Don haka tun da maɓarnatan nan sun tare komai, har ta kai ga ko da kai mutumin kirki ne idan kana cikin jam’iyyunsu ba za ka iya tsinana komai ba, to ya kamata a samu wata tunga daban da za ta tara mutanen kirki,”a cewarsa.

A cewar malamin jami’ar ”Tun 1979 nake malamin jami’a, shekaru 40 kenan yanzu, don haka abun da na karanta da wanda na lura da shi a yayin da nake shugabantar INEC.

“A gaskiya yadda na ga ‘yan siyasarmu na tafiyar da lamarin zabe da kuma yadda suke wakilci idan an zabe su, to gaskiya akwai abun tsoro.”

Tsohon shugaban na INEC ya kara da cewa rashin shugabanci na gari ne ya haifar da dukkan matsalolin da Najeriya ke fama da su, har ta kai ga wasu na neman a raba kasar a halin da ake ciki.

Categories: Uncategorized
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings