X

Ana nuna damuwa kan rashin ji daga iyalai bayan katse layukan waya a Zamfara

Ƴan Najeriya da suka gagara samun iyalansu da ke zaune a Zamfara na cikin damuwa, bayan mahukunta sun toshe layukan intanet da wayoyin hannu.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da jami’an tsaro ke fatattakar ‘yan bindiga da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane domin karɓar kudin fansa.

Katse layukan na da nasaba da bukatar gwamnatin Zamfara ta samun damar daƙile matsalolin tsaro, kuma za a shafe mako biyu cikin wannan yanayi.

Dokar daina samun layukan wayoyi ta soma aiki ne kwanaki bayan garkuwa da dalibai sama da 70 a wata makarantar sakandare da ke garin Kaya-Maradun.

Mahukunta na da yaƙinin cewa katse layukan sadarwar zai taimaka wajen fatattakar ‘yan bindigar da suka addabi yankin.

Sai dai ana kuma nuna damuwa cewa, mai yiwuwa maharan su tsallaka jihohi makwaɓta inda za su iya samun layin waya ko intanet.

Rahotanni na cewa rundunar sojin Najeriya na ta yin luguden wuta a dazukan yankunan Zamfarar inda ake kyautata zaton maɓoyar ‘yan bindiga ce.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings