Wata cacar-baki ta barke tsakanin hedkwatar tsaron Najeriya da dan Majalisar Dokokin jihar Sokoto, kan harin ISWAP da ‘yan bindiga suka kai jihar.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce dakarunta na rundunar Operation Hadarin Daji da sauran jami’an tsaro sun sami nasarar murkushe wani farmakin mayakan ISWAP da ‘yan bindiga dadi, akan wani sansanin sojoji dake Burkusumma dake yankin karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Kakakin hedikwatar tsaron Najeriya, Majo Janar Benjamin Olufemi, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu ya ce ‘yan bindigar sun afkawa sansanin dakarun Najeriya ne wanda ke kan iyakar Najeriya da Nijar, sai an murkushesu.
A cewar hedikwatar tsaron Najeriya, ta ce irin yadda sojoji ke fafarar ‘yan bindigar a ‘yan watannin nan a yammacin Arewacin Najeriya, hakan ya zame wa ISWAP da ‘yan bindigar alakakai, dake zuwa a dandazonsu musamman a yayin da sojojin suka fita sintirin kai farmaki.
Biyo bayan dauki da wasu dakarun su ka kaiwa abokan aikinsu, an murkushe harin tare da halaka dinbin ‘yan bindigar, yayin da wasu masu yawan gaske suka arce da raunin harbin bindiga.
Hedikwatar tsaron ta ce a halin yanzu kuma, sojojin Najeriya da Nijar suna can suna farautar ‘yan ta’addar akan iyakokin kasashen biyu.
A gefe guda kuma, dan Majalisar Dokokin jihar Sokoto mai wakiltar yankin Sabon Birnin, Aminu Mustpha Goza, ya ce ko kadan sojojin ba gaskiya suke fada ba.
Goza ya ce jami’an tsaro bakwai ne suka tsira, kuma yanzu haka ana neman mutane 10. Ya ci gaba da cewa an kai musu gawarwaki sama da 17.
Ya ce duk da cewa akwai gawarwakin sojoji dake asibitoci biyu a Sabon Birni, amma abin mamaki sai ga shi rundunar tsaro ta fitar da sanarwar wai ISWAP ne suka kai harin.
Dan Majalisar ya tabbatarwa da Muryar Amurka cewa ‘yan bindiga ne dake yankin suka kai hare-haren karkashin jagorancin wani da ake kira Tuji, kuma an gansu lokacin da suke shiga kan babura ba tare da an kashe musu ko da mutum daya.