Sojan dake mulki a kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da shawo kan yunkurin juyin mulkin da aka samu Talata kuma rayukan mutane 11 suka salwanta sakamakon yunkurin.
Bayanai na cewa an sami maido da zaman lafiya a birnin Guinea-Bissau kwana daya bayan da shugaba Umaro Sissoco Embalo ya tsallake rijiya da baya.
A ranar Talata data gabata wasu sojoji dauke da manyan bindigogi suka zagaye gidan gwamnati dake Bissau inda Shugaban kasar da kuma Firaminista ke taro.
Shugaba Embalo mai shekaru 49 ya shaidawa manema labarai cewa ya yi katarin tsallake rijiya da baya, bayan kwashe sao’i biyar ana ta barin wuta da niyyar kwace gwamnati.
Majiyoyin soja dake Guinea-Bissau sun shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa sau hudu ana yunkurin juyin mulki tun bayan samun ‘yanci daga Portugal a shekara ta 1974.
A yanzu haka hukumomin kasar sun kaddamar da cikakken binciken yumkurin juyin aikin.