Wannan sabon hari da aka kai a garin Tulsa, ya tayar da hankalin jama’a ganin yadda ake samu wasu jerin hare-hare a makaranta da kuma shagon sayar da kayayyaki a Amirkar.
Rahotannin da ke fitowa daga jihar Oklahoma na kasar Amirka, na cewa wani dan bindiga ya kutsa cikin wani asibiti da ke birnin Tulsa, inda ya yi harbin kan mai uwa da wabi.
‘Yan sanda sun ce dan bindigar ya hallaka akalla mutum hudu, sannan ya kashe kansa, yayin kuma da ake ci gaba da binciken abin da suka ce har yanzu ba su tabbatar da manufar kai harin ba.
Birnin Tulsa dai na da sama da mutum dubu 400 da ke zaune a cikinsa, yana kuma da nisan mil 100 ne daga fadar gwamnatin Oklahoma.
Ko a makon jiya ma wani dan bindiga ya kashe wasu yara ‘yan makaranta su 19 tare da malamnsu biyu a garin Uvalde da ke a birnin Texas, baya ga wani da shi ma ya kai hari wani babban shagon sayar da kayayyaki a birnin New York a cikin watan jiya ya kuma halaka akalla mutum 10.