X

An yanke wa mawaƙi hukuncin kisa ta hanyar rataya a Kano

Wata babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W. tare da wani da ya yi ɓatanci ga Allah. 

Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka ƙara.

“An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka,” in ji Jibo Ibrahim. 

“A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na 382 (b) na kundin shari’ar Jihar Kano ta shekara ta 2000 ta tanada

Tun a watan Maris na 2020 ne Aminu Sharif, mazaunin unguwar Sharifai da ke ƙwaryar birnin Kano ya yi wata waƙa, wadda aka zarge shi da yin ɓatancin a cikinta. 

Kazalika kotun ta yanke wa wani matashin mai suna Umar Farouq hukuncin shekara 10 a gidan yari tare da horo mai tsanani bisa laifin ɓatanci ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Alƙali ya yanke wa Umar Farouq hukuncin ne sakamakon shekarunsa ba su kai 18 kamar yadda kundin manyan laifuka ya tanada. 

Ya yi ɓatancin ne yayin da suke yin ce-ku-ce da wani.

Tun a watan Maris ne matasa suka yi sun yi zanga-zangar neman a hukunta wani Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci.

Matasan sun yi cincirundo ne a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar ya tarbe su.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.Shugaban mutanen da suka yi zanga-zanga a watan Maris, Idris Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa hukuncin zai zama izina ga sauran jama’a wadanda “suke son bin hanya irinta Yahaya”.”Lokacin da na ji hukuncin na ji matukar jin dadi saboda hakan ya nuna cewa ba a banza muka yi zanga-zanga ba. 

“Wannan hukuncin zai zama darasi ga sauran jama’a wadanda ke ganin za su ci mutuncin addininmu da ma’aikin Allah ba tare da an dauki mataki ba,” in ji shi.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings