X

An tura Aminu gidan yari

Wani dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, Aminu Adamu, wanda aka kama bayan ya caccaki uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a shafin Twitter, an tsare shi a Suleja.

Aminu Adamu dalibin jami’ar tarayya dake Dutse, wanda aka kama bayan ya caccaki uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a shafin Twitter, an tsare shi a gidan yarin Suleja dake jihar Neja.

A cikin watan Yuni, dalibin ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Su mama Anchi Kudin Talakawa an koshi”, ma’ana “Mama ta ciyar da kitso akan kudin talakawa”.

Bayan watanni ne jami’an tsaro suka kama shi tare da garzaya da shi zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka yi masa duka da azabtarwa kamar yadda kawunsa ya bayyana.

Daga nan ne aka gurfanar da dalibin a wata kotu da ke Abuja, inda aka hana shi beli duk da cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

An kama wata mai sukar Aisha Buhari, Najatu Mohammed ta tuhumi ‘yan Najeriya
A saki mai sukar Aisha Buhari yanzu, jam’iyyun adawa sun fadawa DSS, ‘yan sanda
Da yake zantawa da BBC Hausa, lauyan CK Agu ya ce, “Ko a zaman kotun da aka yi jiya mun sanar da alkali kokarin da aka yi na ganin an bayar da belinsa, amma ba mu samu amsa daga ‘yan sanda ba. Mun nemi kotu ta bada belin dalibin bisa dalilan lafiya da kuma cewa zai yi jarrabawar ranar 5 ga watan Disamba. Kotun ta umurci ‘yan sanda da su gabatar da bukatar neman beli a gabanta domin tantancewa tsakanin Talata zuwa Laraba,” inji Mista Agu.

Aminu wanda dan asalin garin Azare ne a jihar Bauchi, dalibi ne a matakin karshe a Sashin kula da muhalli a Jami’ar Tarayya dake Dutse.

Kamen nasa dai ya haifar da bacin rai musamman a shafukan sada zumunta, inda ‘yan Najeriya da dama ke cewa babu wanda ya isa a kama shi saboda yada ra’ayinsa.

Iyayen Aminu sun nemi gafarar uwargidan shugaban kasar tare da neman a sake shi. Har yanzu Aisha Buhari ba ta ce uffan ba kan wannan ci gaban.

Categories: Labarai
Tags: labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings