Rundunar ‘yan sanda a jihar Nasarawa da ke Najeriya ta tabbatar da sace Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar Yakubu Lawal.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a ranar Talata a Lafiya, babban birnin jihar.
A cewar jami’in hulda da jama’ar, da misalin karfe 8 da minti 45 na daren Litinin ‘yan sandan da ke sintiri suka rinka jin harbe-harben bindiga a karamar hukumar Nassarawa-Eggon, daga nan suka je wajen.
Ya ce koda suka je wajen sai suka tarar har wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun far wa gidan Kwamishinan Yada Labarai na jihar tare da yin awon-gaba da shi ta karfin tsiya.
Jami’in hulda da jama’a na runudnra ‘yan sandan ya ce tuni aka baza jami’an ‘yan sanda domin ceto kwamishinan.
Ya kuma bayar da umarnin cewa dukkan wanda ya samu labari game da in da aka kai kwamishinan da ya taimaka domin kubutar da shi.
A ranar Asabar din data wuce ma, rahotanni daga karamar hukumar ta Nassarawa-Eggon suka ce wasu in bindiga sun kai hari makarantar sakandiren kimiyya da ke garin inda suka kashe ma’aikaci guda a ciki.