Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayyana cewa kowane maniyyatan aikin hajjin shekarar 2023 zai biya akalla N2.89m.
Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, inda ya danganta hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da Saudiyya.
Hassan ya ce farashin ya kai nau’i 8 da jihohin Borno da Yobe don biyan mafi karancin farashi yayin da Jihohin Legas da Ogun suka fi Naira miliyan 2.99.