X

An kashe mutum hudu, an sace mutum 24 a Harin Chibok

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya ziyarci garin Chibok ranar Litinin bayan wani harin da aka kai kan wasu al’umomi uku na karamar hukumar.

Yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya gana da iyalan mata 22 da maza biyu da mayakan Boko Haram/ISWAP suka sace a Kawtakare, Korohuma da kuma Pemi yayin harin da suka kai. 

Mayakan sun kai wannan harin ne a Kawtakare ranar 21 ga watan Janairu, 2022, inda kuma suka kai wani harin ranar 14 ga watan na Janairu bayan na ranar 30 ga watan Disambar bara da suka kai kan al’ummar Korohuma.

Gwamnan ya ce, “Mun zo Chibok ne domin yi muku jaje, musamman ‘yan uwan wadanda aka sace da ‘yan uwanmu mutum hudun da mayakan Boko Haram suka kashe.”

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta ji zafin al’amarin da ya auku kuma ya yi alkawarin haka ba zai sake aukuwa ba.

Gwamna Zulum ya lura cewa kananan hukumomin Biu da Askira da Chibok da kuma Damboa ne suka fi shan wahalar jerin hare-haren da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP ke kai wa yankin.

Ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta gaza ba wajen bai wa jami’an tsaro taimakon da suke bukata domin kawo karshen wannan al’amarin.

Maharan sun kona gine-gine 110 inji Umar Ibrahim

Yayin da yake nasa jawabin, shugaban karamar hukumar ta Chibok Umar Ibrahim ya ce baya ga mutum 24 da aka sace, da mutum hudun da suka rasa rayukansu, maharan sun kona gine-gine 110, wadanda suka hada da gidaje 73 da shaguna 33 da kuma coci-coci guda hudu.

Akwai kuma motocin hawa takwas da kekuna uku da su ma mayakan suka kona.

Gwamnan na Borono ya umarci karamar hukumar ta tattara bayanan ainihin barnar da aka yi wa al’umomin uku sannan su mika masa cikakken rahoton.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings