Wani harin da aka kai a wani masallaci a gabashin Burkina Faso ya yi sanadin mutuwar musulmi da dama a rana guda .kazamin harin da aka kai kan mabiya darikar Katolika da ke halartar taron jama’a, kamar yadda majiyoyi na cikin gida da na tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a ranar Litinin din nan.“
Mutane dauke da makamai sun kai hari a wani masallaci a Natiaboani ranar Lahadi da misalin karfe 5:00 na safe, wanda ya yi sanadin kashe mutane da dama,” in ji wata majiyar tsaro.“
Wadanda aka kashe dukkansu Musulmai ne, yawancinsu maza ne” wadanda suka zo sallar asuba, kamar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana ta wayar tarho.
Wata majiya a yankin ta ce “’yan ta’addan sun shiga garin ne da sanyin safiya. Sai suka kewaye masallacin, suka harbe muminai, wadanda suka taru a wurin domin yin sallar farko ta wannan rana.”
Majiyar ta kara da cewa “An harbe da dama daga cikinsu, ciki har da wani muhimmin shugaban addini.”
Sojoji da mambobin kungiyar sa kai na tsaron kasar (VDP), wata runduna ce ta farar hula da ke goyon bayan sojoji, “
wadannan runduna da suka zo da yawa sun kai hari”, in ji majiyar guda.Majiyar ta bayyana shi a matsayin “babban hari” dangane da adadin maharan, wadanda kuma suka yi barna mai yawa.
Natiaboani al’ummar karkara ce mai tazarar kilomita 60 (mil 37) kudu da Fada N’Gourma, babban gari a yankin gabashin Burkina, wanda ke fuskantar hare-hare akai-akai daga kungiyoyi masu dauke da makamai tun shekarar 2018.
A daidai wannan rana da harin da aka kai a masallacin, an kashe fararen hula akalla 15 tare da jikkata wasu biyu a harin da aka kai kan wata majami’ar Katolika a daidai lokacin da ake gudanar da taron gangamin ranar Lahadi a arewacin kasar Burkina Faso, in ji wani babban jami’in cocin.
Jean-Pierre Sawadogo, mataimakin shugaban diocese na Dori, ya fada a cikin wata sanarwa cewa “harin ta’addanci” ya faru ne a kauyen Essakane yayin da mutane ke taruwa domin yin sallar Lahadi.Kauyen Essakane yana cikin yankin da aka fi sani da “iyakoki uku” a arewa maso gabashin kasar, kusa da kan iyakokin kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.