Akalla mutane takwas ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon rikici da ya barke ranar Litinin a garin Mangu da ke karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, inji rahoton Daily Trust.
Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya fito daga karamar hukumar da ke fama da rikici, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Mangu da kewaye sakamakon rikicin da ya barke a yankin.
Rahotanni sun nunar da cewa an kashe wasu mutane tare da jikkata wasu da dama ba a iya gano su ba bayan sun tsere daga gidajensu.
Malaman addini da jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnati sun tabbatar da faruwar lamarin, inda wasu majiyoyi ke zargin cewa ya na da alaka da yunkurin satar shanu da aka bijire, lamarin da ya haifar da tarzoma.
Sai dai mai baiwa gwamnan jihar Filato shawara kan harkokin tsaro, Birgediya Janar Shipi Gakji mai ritaya ya danganta rikicin na ranar Litinin da sabani kan hakkin hanya.
A cewarsa: “Abin da ke faruwa a Mangu a halin yanzu ya samo asali ne sakamakon rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin bangarorin biyu wanda ya ta’azzara. Amma jami’an tsaro suna nan a kasa suna kokarin ganin sun daidaita komai.
Duk da haka, irin wadannan abubuwan da suka faru, ’yan iska da miyagu sun yi kokarin yin amfani da damar wajen haifar da tarzoma, wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da suka kara ta’azzara kuma suka kai ga kafa dokar ta-baci a Mangu,” in ji Janar Gakji.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan daga bangarorin biyu sun kona gidaje da masallatai da coci-coci.
Da yake nasa jawabin mataimakin shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) reshen karamar hukumar Mangu, Malam Adamu Abdulsalam, ya shaida wa wakilinmu a jiya cewa an kona masallatai shida ciki har da masallacin Juma’a na Anguwan Dawo a lokacin da lamarin ya faru.