Yan sanda da hukumomin lafiya a Brazil sun dakatar da wasan share fage na cin kofin duniya da kasar ke bugawa da Argentina, da nufin kama wasu yan wasan Argentina hudu da suka saba dokar kullen Korona.
Yan wasan sun hada da Lo Celso da Romero da Martinez da Buendia da dukansu ke wasa a Ingila.
An zarge su da kin killace kansu duk da cewa sun fito daga yankin kasashen da Brazil ta ayyana mafiya hadarin kamuwa da cutar Korona nau’in Delta.
Hukumomin sun kutsa kai filin jim kadan bayan fara wasa, suka kuma bukaci a basu yan wasan su wuce dasu.
Sai dai hakan ya haifar da sa-in-sa, wadda tasa duka yan wasan Argentina suka yanke shawarar ficewa daga filin.
Rahotanni na cewa sun nuna cewa ‘yan wasan ba su fadi cewa suna Ingila ba kasa da mako biyu da suka wuce, wanda kuma hakan ya saba wa dokokin killace kai na Brazil.