X

An kama wani matshi bayan ya fille kan ‘yar uwarsa mai juna biyu

‘Yan sanda a birnin Maharashtra na yammacin Indiya sun kama wani matashi da ake tuhuma da datse kan ‘yayarsa wadda ke da juna biyu.

Jami’ai a yankin na cewa matar mai shekara 19 da haihuwa ta auri wani mutum ne ba tare da amincewar ‘yan uwanta ba.

Tana cikin hada wa dan uwanta da mahaifiyarta shayi ne sai kwatsam aka kai ma ta wannan mummunan harin da lauje. Daga baya matashin da mahaifiyarsa sun mika kansu ga ‘yan sanda.

‘Yan sanda sun ce suna tuhumarsau da daukar hoto da kan matar da suka datse.

Wannan aika-aikar ta auku ne a gundumar Aurangabad inji Sashen Marathi na BBC.

A watan Yuni ne matar ta tsere daga gida kuma ta auri masoyin nata duk da rashin amincewar ‘yan uwanta. Duk da cewa kuma angon ya fiti ne daga bangare irin nasu, amma ba su amince masa ba saboda ‘yan uwansa ba su da kudi kamar ‘yan uwan amaryar.

Masu fafutukar kare hakkin dan Adam na cewa akan kashe daruruwan mutane a Indiya a kowace shekara saboda sun ki bin umarnin ‘yan uwansu wajen auren wadanda suke so.

A watan Maris, ‘yan sanda a jihar Uttar Pradesh ta arewacin Indiya sun kama wani mutum da suke tuhuma da datse kan ‘yarsa, kuma ya shaida wa ‘yan sandan cewa ya kashe ta ne saboda ta auri wani mutumin da bai amince da shi ba.

Categories: Labarai
Tags: HAUSAlabarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings