Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Nasarawa ta sanar da kama mutum 50 wadanda ta ke tuhuma da satar mutane a jihar.
Cikin wani rahoto da jaridar The Nation ta wallafa, ta ce Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Adesina Soyemi, wanda ya nuna wa jama’a mutanen da ake tuhumar a Lafia babban birnin jihar, ya ce an kama su ne a wurare daban-daban cikin jihar.
Ya kara da cewa an kama wasunsu ne saboda aa tuhumarsu da kashe shanu 29 ta hanyar basu guba, wasunsu kuma an kama su ne kan tuhumar gama baki da wasu domin su aikata miyagun laifuka, da zama mambobin kungiyoyin asiri da kuma aikata kisan kai.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma ce jami’ansa sun kama wasu mutum 11 da ake tuhumar suna aikata fashi da makami.
A jihar Ogun da ke kudu maso yammacin kasar, ‘yan sanda sun nuna wa jama’a wasu mutum 52 da ake tuhuma da zama mambobin kungiyoyin asiri da tayar da hankulan al’ummar jihar.