Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun ce daga shekara ta 2015 zuwa farkon wannan shekarar, kasar ta kama miyagun kwayoyi iri daban daban da aka kiyasta kudinsu ya haura cfa milyan dubu 93.
A taron manema labaran hadin gwiwa da suka gabatar jiya Litinin a birnin Yamai, minista kuma kakakin gwamnatin kasar ta Nijar, Tidjani Abdoul Kadiri da takwaransa na cikin gida Hamadou Souley, sun bayyana cewa yanzu haka akwai mutane da dama da ke tsare saboda zargin fataucin wadannan kwayoyi.