X

An kama daruruwan mutane da ke zanga-zanga a Faransa

Mutane 667 ne aka kama cikin dare a Faransa, a cewar Ministan harkokin cikin gida Gerald Darmanin, bayan zanga-zangar da ta barke a dare na uku a jere a fadin kasar, sakamakon harbin wani matashi da ‘yan sanda suka yi a farkon mako.

Hukumomin kasar na hasashen barkewar zanga-zangar har nan da kwanaki masu zuwa sakamakon mummunan harbin da aka yi wa matashin, yayin da a bangare guda suke kokarin shawo kan rikicin da ke dada ta’azzara inda aka dakatar da zirga-zirgar ababen hawa tare da sanya dokar hana fita.

A wata takardar bayanin tsaron cikin gida da aka fitar, ana sa ran a lokutan “dare masu zuwa” za a fuskanci tashin hankali tare da barnata wasu kayayyaki a birnin inda za a fi mai da hankali kan jami’an tsaro da wasu muhimman alamomi a birnin”, a cewar wata majiya ta ‘yan sanda a yammacin ranar Alhamis.

Tuni dai aka ayyana dokar hana fita da daddare a unguwar Clamart da ke Paris, tsakanin karfe 9:00 na dare [1900 GMT] zuwa 6:00 na safe daga ranar Alhamis har zuwa Litinin mai zuwa.

A wani mataki na bayyana irin tashin hankali da aka shiga, an gudanar da tattakin don tunawa da Nahel M. dan kimanin shekaru 17 da ‘yan sandan suka kashe.

Bayan haka ne rikici ya barke inda ‘yan sanda suka yi ta harba barkonon tsohuwa yayin da aka kona motoci da dama a unguwar da aka kashe matashin.

Faransa na fama da zanga-zanga bayan harbe Nahel, wanda aka nada a bidiyo lamarin da ya fusata al’umma tare da tafka muharawa kan aikin ‘yan sanda

“Dole ne duniya ta ga cewa mun yi tattaki kan abin da aka yi wa Nahel,” in ji dan gwagwarmaya Assa Traore, wanda dan uwansa ya mutu bayan an kama shi a shekarar 2016.

Dubban ‘yan sanda ne suka bazu a kan tituna

An tuhumi dan sandan da ake zargi da harbin Nahel a Nanterre da laifin kisan kai da son rai, kuma yana tsare a gidan yari, sai dai ana jira a ga irin tasirin da hakan zai iya haifar da tarzoma da ta barke.

An baza ‘yan sanda kusan 40,000 don kokarin samar da zaman lafiya a ranar Alhamis, fiye da adadin da ke kasa a ranar Laraba, inda aka kama mutane da dama.

An kona motoci da tantuna a daren Alhamis a wasu sassan kasar, yayin da aka kama mutane 150 a fadin kasar bayan barkewar rikicin da ya haifar da kona motocin dakon kaya a wata unguwa da ke birnin Paris.

Za a dakatar da ayyukan bas-bas na Paris da na kananan jirgin kasa bayan karfe 9:00 na dare (1900 GMT) ranar Alhamis, a cewar shugaban yankin.

Shugaba Emmanuel Macron ya yi kira da a kwantar da hankula kuma ya ce tashin hankalin da aka yi a zanga-zangar “bai dace ba”.

Rikicin dai ya yi matukar damun Macron wanda ke kokarin farfadowa daga mumnunar zanga-zangar da aka kwashe tsawon lokaci ana yi kan garambawul din tsarin fansho da ya yi a kasar.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings