X

An kai hari fadar shugaban Guinea-Bissau

Rahotannin daga kasar Guinea-Bissau da ke a yankin yammacin Afirka, sun ce an yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Umaro Sissoco Embalo.

Rahotannin sun ce wasu ne dauke da makamai suka afka wa fadar shugaban kasa da yammacin Talata, inda suka kwashe sa’o’i biyar suna bude wuta.

Masu tsaron fadar shugaban na Guinea-Bissau sun maida martani, abin da ya sanya da dama daga cikin su suka mutu.

Shugaba Sissoco Embalo, wanda ya ce an yi niyyar kashe shi ne tare da mukarrabansa, ya ce an shawo kan lamarin, tare da bayanin cewa an kama wasu daga cikin wadanda suka yi kokarin kwace ikon.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi kiran da a girmama tsarin dimukuradiyya a kasar ta Guinea-Bissau.

Ita ma kungiyar ECOWAS ta yammacin na Afirka wadda ke fama da juye-juyen mulki uku cikin watanni 18, ta nuna damuwarta da faruwar lamarin.

Domin sanya Talla ko kuna son a saka muku Labari

info@twinsempire.com

+2347034512323

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings