An gurfanar da wani mutum gaban kotu bisa zargin sanya hoton bidiyon yara a kafar sada zumunta.
Yaran dai dalibai ne na wata sakandire da ke Lagos.
Sanya bidiyon dai ya janyo suka da kuma kiran a rufe makarantar saboda zargin batsalar da daliban suka yi a yayin wata tafiya karin ilimi da suka yi.
An zargi Uche Igwe, da yada hoton bidiyon daliban makarantar Chrisland.
Yaran dai sun yi abubuwan da basu dace ba a yayin tafiyar da suka yi.
A yanzu dai ya musanta cewa yana da laifi, kuma an bayar da belinsa, sannan an dage sauraron shari’ar zuwa 13 ga watan Mayun 2022.
Gwamnatin Lagos dai tun a baya tayi gargadi a kan duk wanda aka kama ya sanya hoto ko bidiyon yara da ya shafi batsa to zai fuskanci hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara 14.