X

An Gudanar Da Taron Mababbantan Addinai a Jos

Hoton VOA

Mai martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar ya jaddada cewa duk wadanda ke daukan makami suna kisan jama’a da sunan addini, zasu fuskanci mummunan hukunci daga Allah.WASHINGTON DC — 

Sarkin na Musulmi da Shugaban kungiyar hadin kan mabiya addinin kirista da suke shugabantar kungiyar dake sasanta tsakanin mabambantan addinai a Najeriya sun je Jos, fadar jahar Filato ne don yin jaje wa al’ummar jahar kan rikicin da ya rutsa da rayukan jama’a da dama a wassu sassan jahar.

Mai martaba ya nanata cewa idan har gwamnati bata dauki matakin hukunta wadanda ke da laifi ba, to lallai zasu ci gaba da kisan mutane da basu ji ba basu gani ba.

Shugaban kungiyar CAN, Samson Olasupo yace burinsu shine tabbatar da zaman lafiya da hada kan jama’a.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha yace gwamnati zata yi adalci wajen gurfanadda masu laifi a gaban kuliya su fuskanci hukunci.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings