Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta sanar cewa an gama gyara kan hanyar jirgin kasa da ta taso daga Abuja zuwa Kaduna wadda mayakan kungiyar Ansaru ta kai wa harin bam.
Injiniya Fidet Okhiria, wanda shi ne shugaban kamfanin sufurin jirgin kasa na Najeriya NRC, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta ce Injiniya Niyi Ali ne ya sanya hannu kan sanarwar a madadin shugaban kamfanin na NRC:
“An kammala hada hanyar jirgin mai suna AKTS. Wannan na nufin an hada dukkan muhimman bangarorin hanyar baki dayansu.
An kuma gyara bangaren kudu na hanyar jirgin wadda bam ya lalata baki dayanta, inda aka hada ta da bangaren da ke arewaci cikin nasara. An kammala gyaran hanyar jirgi daga Abuja zuwa Kaduna ke nan.”
Injiniyan ya kara da cewa za a fara jigilar jama’a nan ba da jimawa ba, amma za a samar da karin matakan tsaro.
“Za mu bukaci dukkan matafiya su nuna mana lambarsu ta dan kasa kafin mu bari su sayi tikitin jirgin.”
Har zuwa wannan lokacin da ake wallafa wannan rahoton, fasinjojin da aka sace daga jirgin, wadanda kuma ake garkuwa da su, na hannun ‘yan bindiga amma sun sako mutum guda a kwanakin baya. Sun kashe mutum tara yayin da suka kai mummunan harin.