Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi karin haske kan ‘yan bindigar kungiyar Ansaru 250 da ta yi ikirarin kashewa a samamen da suka kai Kaduna da ke arewacin kasar.
Ranar Laraba rundunar ‘yan sandan Najeriya mai yaki da ‘yan fashi ta Operation Puff Adder ta ce jami’anta sun kai hari a dajin Kuduru da ke Birnin Gwari a jihar ta Kaduna tare da taimakon sojojin sama.
Sai dai ta kara da cewa an harbi wani jirginta mai saukar ungulu a lokacin samamen.
Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar ranar Alhamis ta ce jami’anta sun kashe wasu hatsabiban ‘yan fashin daji da masu satar shanu da garkuwa da mutane da take nema ruwa a jallo.
‘Yan fashin su ne Haruna Basullube da Bashir Leta.
Rundunar ‘yan sandan ta ce jami’anta sun kuma yi wa wani kwamandan kungiyar Boko Haram, Malam Abba da wani hatsabibin mai garkuwa da mutane, Mofa, mummunan rauni
A cewarsu, an kwace bindigogi kirar AK47 da daruruwan harsasan manyan bindigogi masu jigida da kakin sojoji da manyan kwalayen kwayar Tramadol da wasu na’urori daga sansanonin.
Rundunar ‘yan sandan ta kuma tura jami’ai na musamman domin zurfafa bincike ta hanyar zamani kan ayyukan kungiyoyin da mukarrabansu.
A lokacin arangamar ne ‘yan bindigan suka harbi jirgin ‘yan sanda, sannan wani jami’in dan sanda ya gamu da ajalinsa yayin da wasu 13 suka samu rauni.
Da yake mika ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, shugaban ‘yan sandan kasar ya jaddada aniyar rundunar ta bayar da kariya ga jami’anta da ma kasar baki daya.
Rundunar ta kuma bukaci mazauna yankin Birnin Gwari a jihar Kaduna da su kai wa ‘yan sanda rahoton duk wanda suka gani da raunin albarushi ko ba su yarda da take-takensa ba.