Majalisar dokokin kasar Habasha ta amince da dage dokar ta-baci inda Amirka ta yi maraba da matakin janye dokar ta-bacin.
Kasar Amirka ta yi maraba da matakin gwamnatin kasar Habasha na kawo karshen aiki da dokar ta baci a kasar sannan ta nemi nan take a saki mutanen da aka garkame karkashin dokar.
A wannan Talata da ta gabata majalisar dokokin kasar Habasha ta amince da dage dokar ta baci da ake aiki da ita a kasar tun watan Nuwamba lokacin da mayakan yankin Tigray suka yi yunkurin kutsawa domin kwace birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar.
Fiye da shekaru guda aka kwashe ana fada tsakanin bangarorin biyu na Habasha bayan Firaminista Abiy Ahmed ya tura dakaru bayan wani hari kan sojojin kasar.