X

Amurka ta kammala ficewa daga kasar bayan shekara 20

Tuni Taliban ta bayyana cewa ta karbi ragamar tafiyar da filin jirgin na Kabul a karon farko bayan shekaru 20

Rukunin ƙarshe na sojojin Amurka da suka shafe shekaru 20 suna yaƙi ya kammala ficewa daga Afghanistan.

Jakadan Washington a Kabul Ross Wilson da kuma kwamandan sojojin Amurkar a can Janar Chris Donahue na cikin jirgin sojin na karshe da ya bar Kabul ranar Litinin da daddare.

Wakiliyar BBC da ke Kabul ta ce duk yinin Litinin shawagin jiragen Amurka kawai ake ji a sararin samaniyar Kabul, yayin da suke bai wa tawagar karshe ta sojojin kariya a kokarin ganin sun bar Kabul.

Tuni Taliban ta bayyana cewa ta karbi ragamar tafiyar da filin jirgin na Kabul.

Baya ga sojojinta, Amurka ta ce ta kwashe fararen hula kusan dubu 80, kuma a yakin da ba ta taba yin mai tsawon shi ba a tarihi, ta rasa sojoji sama da 2,400.

A gefe guda, kungiyar Taliban ta ce yanzu ne Afghanistan ta zamo kasa mai cikakken ‘yanci.

Kungiyar ta yi wannan kalami jim kadan bayan kammala ficewar kason karshe na sojojin Amurka daga Kabul.

Hotunan bidiyo sun nuna mayakan kungiyar na harbi a sama domin murna.

Amma kasashen duniya sun bukaci Taliban ta cika alkawuran da ta dauka na sauyawa daga tsaurin da aka santa da shi a baya.

Sai dai kuma da dama na fargabar da wahala a ga wani sauyi a kasa, yayin da ake ci gaba da ficewa da tsoron Taliban za ta hukunta wasu yan kasar da suka yi aiki da yan kasashen waje wurin murkushe ta a baya.

A nasa bangaren sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya ce sun bude wani shafi a Afghanistan wanda Amurka za ta yi amfani da diflomasiyya wurin kawo mata ci gaba.

Mr Blinken ya ce idan har za su iya aiki kafada da kafada da Taliban domin ganin ci gaban Afghanistan a shirye suke.

Sakataren harkokin kasashen wajen ya ce Amurka za ta ci gaba da taimakawa al’ummar Afghanistan da kayan more rayuwa, amma ta hannun kungiyoyin agajin kasa da kasa ba Taliban ba.

Idan anjima ne Shugaba Joe Biden zai yi wa al’umma jawabi kan matakinsa na kawo karshen yaki a Afghanistan.

Tunda farko Majalisar Dinkin Duniya ta amince da kudurin hana Taliban ba da mafaka ga yan ta’adda, tare kuma da martaba alkawuran da ta dauka da suka hada da kare yancin mata da tsiraru.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings