Wani yaro dan shekara uku ya mutu yayin da dan uwansa dan shekara biyu ya samu munanan raunuka sakamakon mamakon ruwan sama da ya yi barna a garin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye…
Ruwan sama da aka kwashe sama da sa’o’i biyar a karshen mako ya haifar da ambaliya da ta kai ga rugujewar daya daga cikin katangar dakin da yaran biyu ke kwana a ‘Unguwar Fada,’ kusa da fadar Sarkin.
Tuni dai aka binne gawar marigayin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, yayin da aka garzaya da kaninsa da ya samu munanan raunuka zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FTH) da ke Gombe domin yi masa magani. Aminiya ta ruwaito cewa wasu da dama da suka samu raunuka daban-daban suna karbar magani a babban asibitin Bajoga da sauran wuraren kiwon lafiya. Wani mazaunin garin Bajoga mai suna Yahaya Haruna ya shaida wa Aminiya cewa an fara ruwan saman ne da misalin karfe 5:30 na safe har zuwa karfe 11 na safe, inda mutane da dama suka samu raunuka yayin da sama da gidaje 100 da dabbobi da kuma dukiyoyi na miliyoyin naira suka salwanta, akasarinsu. a yankunan Shara-Mansur da Bodoriyel na garin. A lokacin mika wannan rahoton, shugaban hukumar ceto na hukumar bada agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Muhammad Garba, ya ce har yanzu suna nan a garin Bajoga “suna isa wurin domin sanin adadin wadanda suka mutu da kuma adadin gidaje da dabbobi da dukiyoyi da aka lalata. ta hanyar ambaliya.” A halin da ake ciki, gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya jajantawa iyalan mamacin da duk wadanda suka samu raunuka ko kuma suka rasa dukiyoyinsu. A wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ismaila Uba Misilli ya fitar, gwamnan ya umarci ma’aikatar kula da muhalli ta jihar, SEMA da hukumomin yankin da su tantance irin barnar da aka yi a yankunan da lamarin ya shafa, tare da bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Ya tabbatar da kudurin gwamnatinsa na taimaka wa iyalai da abin ya shafa, ya kuma bukaci jama’ar jihar da su yi biyayya ga gargadin afkuwar ambaliyar ruwa, “kuma su guji wuraren da ke fama da ambaliyar ruwa a matsayin matakin kariya.”