Jami’an agajin gaggawa a lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar China sun ce akalla mutum shida suka mutu bayan ambaliyar ruwa ya yashe bangaren wani kauye a jiya Asabar.
Ba a kuma ga wasu mutum 12 ba ya zuwa yanzu. Hotunan bidiyo na inda lamarin ya faru sun nuna jami’in agaji na daukar wata dattijuwa cikin mamakon ruwa, wasu kuma na rakuɓewa gefen wani tsauni domin tseratar da rayukansu.
Mamakon ruwan sama ya shafi mutane kusan 20,000 a yankin .