Mallam Abubakar Yunus wanda aka kashe ’ya’yansa biyu a harin ya ce tare da shi aka kama su kuma a kan idonsa aka yanka su.
“Mutane na aiki a gonakinsu. A gonarmu abun ya fara ne misalin karfe 10.30 na safe lokacin da mayakan Boko Haram dauke da bindigogi sanye da kayan sojoji suka yi mana kawanya.
“A gabana suka yanka ’ya’yana bayan da daya daga cikin mayakan ya tambaye ni matsayin yaran a wurina! Na amsa da cewa ’ya’yana ne.
“Har yanzu ina cikin tashin hankali game da irin wannan rashin imani da aka nuna min”, inji shi.
An gama da majiya karfin yankin
Wata majiya ta ce an kawar da akasarin matasa da majiya karfin yankin yanzu saura ’yan tsiraru.
“Matasa ne majiya karfi da wadanda za su kula da wannan al’umma a nan gaba aka karkashe.
“Ba za mu taba farfadowa ba saboda karni guda na al’umma ne sukutum aka shafe aka bar mu tsofaffi, mata da kananan yara masu rauni”, inji shi.
Wakilinmu ya ce manoman da suka hada da mata da kananan yara, suna taska da girbin shinkafa ne aka yi musu kawanya da misalin karfe 9 na safe ranar Asabar, a Zabarmari mai tazarar kilimita 25 daga Maiduguri, hedikwatar Jihar Borno.
Sai daga baya a ranar Lahadi aka samu karin bayani game da yadda aka karkashe rukunin farko na manoman.
Rahotanni sun ce sai da mayakan suka tisa keyarsu da bakin bindiga zuwa wani wuri sannan suka rika yi musu yankan rago da fille kai.
Bayan sun karkashe rukunin farko na manoma 43, sai mayakan suka yi ta banka wa gonakin da ke yankin wuta.
Hakan ya hana jami’an tsaro da ’yan sa kai isa ga wurare masu makwabtaka da Zabarmari domin ganin halin da suke ciki, a cewar majiyoyinmu.
Dalilin kai wa manoman shinkafa hari
Mazauna sun ce tun ranar Alhami da Juma’a mayakan Boko Haram daga bangaren Abubakar Shekau suka shiga Zabarmari suna kwatar kayan abinci da suran abubuwa daga hannun mazauna kauyuka.
“Yana daga cikin salon ’yan ta’addan kwace wa kauyawa abinci, kudade da sauran abubuwan bukata da bakin bindiga” inji wata majiya da ke da masaniya kan dabi’ar kungiyar.
“Sai dai rana ta baci wa daya daga cikin ’yan ta’addan da ya je Zabarmari ranar Juma’a ya tursasa wasu iyalai su dafa masa abinci ya kai wa ’yan uwansa.
“Iyalan sun amince amma da ya shiga bayi sai kauyawan suka yi ta maza suka dauke bindigarsa, da ya fito suka kama shi suka damka shi a hannun jami’an tsaro”, inji majiyar.
Wata majiyar kuma ta ce karfin halin da kauyawan ba su taba yin irinsa ba ne ya fusata ’yan ta’addan suka taru bayan awa 24 suka yi wa manoma dirar mikiya a lokacin da suke tsaka da aiki a gonakin shinkafa.
“Manoman shinkafa 43 da aka binne [ranar Lahadi] an yi musu kawanya ne a wuri guda, aka dauke su zuwa wani wuri mai nisan kilomita 10 daga zabarmari aka kulle su a wani daki.
“Biyu-biyu, uku-kuku aka rika kiran su, ’yan ta’addan na musu tambayoyi kafin su daure musu hannayensu a baya su yanka su, wasu kuma fille kawunansu aka yi, aka dora kawunansu a kan gawar.
“Wannan shi ne kololuwan rashin tausayi saboda ’yan kalilan daga cikin wadanda da aka kama ne kadai aka kyale”, a cewarta.
Mun sanar wa sojoji amma suka yi biris da mu
Wani daga cikin manoman da ya tsira, Abubakar Salihu ya ce tun lokacin da aka kama dan Boko Haram din da aka damka wa jami’an tsaro suke fargabar za a kawo musu hari.
“Tun da wuri muka sanar da sojoji cewa mu ga ’yan Boko Haram masu yawan gaske, amma babu abin da aka yi a kai.
“Abin takaici ne ga Zabarmari, da an kawar da aukuwarsa amma sojoji suka ki su dauki mataki kan bayanan da muka ba su”, inji majiyar.
Wani manomi garin, ya ce, mamatan na cikin aikin girbin shinkafa ne mayakan suka kira su suka tara su a wuri guda.
“Da gangan suka yi hakan don su hana mu girbe amfanin gonarmu; Muna rokon Gwamnatin Tarayya ta taimaka ta kare mana rayukanmu”, inji shi.
Kimanin mako biyu da suka wuce sojoji da ’yan sa kai sun kama wasu mayaka na Boko Haram a yankin.
Muna cikin tashin hankali —Zulum
Da yake ta’aziyya ga al’ummar Zabarmari, Gwamna Babagana Zulum, ya ce: “Ina kara jajanta muku game da wannan mummunan rashi da ya same mu baki daya da duk wani mutum mai tausayi.
An shaida min cewa har yanzu akwai wadanda ba a gani ba kuma tun jiya [Asabar] muke magana da sojoji, in Allah Ya yarda za a gano su.
“Abin takaici ne a ce an yi wa fiye da mutum 40 yankan rago daga gonakin da suke aiki.
“Mutanenmu na cikin tsaka mai wuya ta fuska biyu: idan suka zauna a gida yunwa ta kashe su; idan kuma suka je gona Boko Haram ta kashe su.
“Wannan abun takaici ne matuka. Muna rokon Gwamnatin Tarayya ta dauki karin matasan sa kai na CFJT da mafarauta a aikin soja da Civil Defence don a sa su cikin jami’an tsaro masu kare gonaki da manoma.
“Akwai tsananin bukatar jami’an tsaron gonaki kuma matasanmu sun san yanayin yankin; ba mu yanke kauna ba, muna da kyakkyawan fata cewa za a kawo karshen wannan ta’addanci”, inji Zulum.
Adalin manoman da kungiyar Boko Haram ta yi wa kisan gilla ranar Asabar a Zabarmari, Jihar Borno ya karu zuwa 110.
Ofishin Majalaisar Dinkin Duniyan ne ya sanar da haka ranar Lahadi bayan jana’izar 43 daga cikin manoman shinkafar da aka fara gano gawarwarkinsu bayan iftila’in na kauyen Koshebe da ke Karamar Hukumar Jere.
Da yake nuna kaduwa da kashe manoman, jami’in Ofishin na Najeriya, Edward Kallon, a cikin sanarwar ya ce ragowar gawarwakin da suka kai adadin ga 110 an gano su ne a warwatse.
Da farko an gano gawa 43 da kungiyar ta fille wa sasunsu kai wasu kuma ta yi musu yankan rago bayan ta kama su a gonaki.
A ranar Lahadi a lokacin jana’izar wadanda aka fara ganowan, hukumomi a Jihar Borno sun ce za a binne karin wasu gawarwakin daga baya.
Garin Zabarmari inda aka binne manoman ya girgiza matuka inda dangi da makusantan mamatan suka yi ta juyayi da nuna kaduwa.
Jama’a a sassan Najeriya sun bayyana fushinsu game da yadda ake karkashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a sassan kasar.
Sun yi ta amfani da shafukan zumunta wajen yin tir da harin Zabarmari tare da kiran gwamnati ta gaggauta daukar matakin kawo karshensa.
Kisan Zabarmazi na zuwa ne bayan an mako biyu ’yan bindiga na garkuwa da mutane da kashe-kashe a sassan Najeriya inda abin ya fi tsanani a yankin Arewa.
A jawabinsa kan lamarin, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III ya ce yanzu yankin Arewa ne wuri mafi hatsari ga rayuwa a Najeriya.
Ita ma Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) da takwararta ta Yarabawa (Afenifere) sun yi tir da hare-haren tare da kiran gwamnati da ta kare jama’ar kasar.
A nasa bangaren, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa manoman.
Sanarwar da kakakinsa, Garba Shehu ya fitar ta ce shugaban ya ba da duk goyon baya da gudunmuwa ga dakarun gwamnati don kare Najariya da jama’ar kasar.