Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa a bana ta ƙudiri aniyar kai shirin nan na ciyarwa a makarantu (National Home Grown School Feeding Programme, NHGSFP) zuwa mataki na gaba.
Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ita ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka mata a harkar yaɗa labarai, Halima Oyelade, ta bayar a Abuja.
A cewar Sadiya, ma’aikatar ta, tare da taimakon Hukumar Abinci ta Majalisar Ɗinkin Duniya (World Food Programme, WFP), za ta yi amfani da shirin wajen yaƙi da yunwar da ƙananan yara ke fuskanta a Nijeriya.
Ta yi bayanin cewa a wannan matakin, za a haɓaka tattalin arzikin jama’a kuma a ƙara yawan yaran da ake ɗauka a makarantun firamare tare da tabbatar da cewa su na zuwa makaranta a kullum.
Ta ce: “Sakamakon da aka samu daga wani nazarin haɗin gwiwa da aka yi a farkon shekarar 2021 don a gano hanyoyin da za a inganta tare da haɓaka shirin na NHGSFP ya nuna cewa an samu nasara sannan akwai buƙatar a kyautata shi sosai domin samun ƙarin tasirin shi.
“Shirin ya na taimakawa wajen inganta abinci, ilimi da kyawawan ɗabi’un cin abinci, kuma ya na bada ƙwarin gwiwar samar da kayan abinci iri daban-daban, musamman namu na gargajiya.
“Hukumar WFP ta na mara wa mataki na gaba baya ta hanyar kawo kayan aiki na sadarwar zamani irin su komfuta. Wannan ya haɗa da ƙananan komfutoci da aka haɗa su da manhajar ‘PLUS Schools Menus’ – wanda ana bada ita kyauta ne domin taimaka wa jami’an kula da abinci su tsara jadawalin abincin da ake ci a makarantu.
“Kayan aikin za su taimaka wa ƙoƙarin da ma’aikatar ke yi wajen saka tsare-tsaren ta na sanya ido da kuma nazarin ayyukan ta a cikin na’urar komfuta, kuma zai ƙarfafa wa shirin ƙasa bai-ɗaya na tsarin ‘PLUS School Menu Tool’ wanda hukumar WFP ta ƙirƙira don inganta sassauƙan jadawalin cin abinci.”
Ministar, har ila yau, ta yi bayanin cewa ya zuwa shekarar 2021, wannan sabon shiri ya bayar da abinci ga yara ‘yan makaranta sama da miliyan tara a makarantun firamare na gwamnati 53,000, wanda hakan ya sa shirin ya kasance ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen ciyarwa a makarantu mafi girma a nahiyar Afrika.
Hajiya Sadiya ta ce shirin ya kuma taimaka wajen yawaitar yaran da ake ɗauka a makaranta a duk faɗin ƙasar nan.
Ta ƙara da cewa shirin ya samar da cigaba matuƙa wajen haɓaka tattalin arzikin jama’a ta hanyar sayen kayan abinci da ƙananan manoma ke nomawa da kuma samar da aikin yi ga sama da masu dafa abinci 107,000 daga iyalai marasa galihu.
Ta ce, “Makarantun sun sama wa ƙananan manoma tabbatacciyar kasuwar sayar da kayan da su ka noma, wanda hakan ya samar da kuɗin shiga da kuma zummar ƙara zuba jari da yin aiki tuƙuru.
“Yaran su kan samu abinci mai lafiya kuma kala-kala; wannan ya sa za su fi zama a cikin makaranta su yi karatu sosai fiye da da, kuma su inganta abin da za su iya zama idan sun girma.
“Kamar yadda ɗaya daga cikin burukan gudanar da shirin ciyarwar na NHGSFP ya tanadar, an yi haɗin gwiwa mai yawa da ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati da su ka dace.
“A gaskiya hakan ya ƙarfafa cuɗanya da haɗin gwiwa da ake buƙata don cimma nasarar aikin da aka sa a gaba.
“Manyan hukumomin da aka yi haɗin gwiwar da su sun haɗa da NYSC, Ma’aikatun Aikin Gona, Ilimi, Yaɗa Labarai, Kasuwanci Da Zuba Jari, da Albarkatun Ruwa.”
Bugu da ƙari, ministar ta ce shirin ciyarwa na NHGSFP muhimmin tsarin agaji ne na gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Ta ce, “Ta hanyar shi, ana iya tunkarar matsalolin yunwa, rama, fatara, rashin aikin yi, ilimi, da sauran su. Shiri ne wanda Gwamnatin Tarayya ke ɗaukar nauyin sa kacokam saboda girman alfanun sa a matsayin sa na hanyar kawo cigaban al’umma.
“Mu a Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa mu na nan cikin shiri a ko yaushe don tabbatar da cewa wannan shiri ya ƙarfafa kuma ya ɗore saboda ya ci gaba da taimaka wa buƙatun ƙananan yara da iyalai da al’ummomi waɗanda domin su aka yi shi.
“Don haka, taimakon da hukumar WFP za ta bayar ya zo a kan kari, ya dace, kuma mu na murna da shi matuƙa.’’