X

A Amurka ana ta ce-ce-ku-ce kan dokar hana zubar da ciki ta Texas

Jihar Texas ta Amurka ta yi dokar da ta haramta wa mata zubar da cikin da ya kai sati shida, inda dokar wadda ta haifar da takaddama ta fara aiki bayan da kotun kolin kasar ba ta saurari karar da aka daukaka a kai ba.

Dokar wadda tana daya daga cikin ire-irensu da suka fi takurawa tun bayan halatta zubar da ciki a fadin Amurka a 1973, ta fara aiki ne bayan da kotun kolin Amurkar ba ta amsa bukatar masu rajin kare hakkin mata na zubar da ciki ba kan daukaka karar da suka yi a kai.

Shugaba Joe Biden kamar sauran kungiyoyin kare hakkin mata da likitoci suna suka, inda ya ce dokar karara ta take hakkin da kundin tsarin mulkin kasar ya bayar, abin da gwamnatinsa ke hankoron tabbatarwa.

Yanzu dai da wannan doka Texas ta zama jihar Amurka da yake da wuya mace ta samu damar zubar da juna biyu.

Domin dokar ta haramta matakan da ake bi tun ma kafin mata da dama su san suna da ciki – wanda shi ne daidai lokacin da za a iya jin alamar bugawar zuciyar dan tayi, wanda shi ne daga kusan mako na shida.

Masu ayyukan da suka jibanci zubar da ciki da kuma kungiyoyi masu goyon bayan zubarwar, suna kokawa da cewa dokar kusan za ta haramta zubar da duk wani juna biyu a Texas, da kuma sa cibiyoyi da ke aikin rufewa.

Shugaban Amurkar Joe Biden ya soki dokar da cewa ta saba wa tsarin mulkin kasar, yana mai cewa hukuncin da aka taba yi a 1973 na Roe v Wade ya bayar da ‘yancin zubar da ciki har lokacin da ciki ya kai mako na 24.

Shugaban ya kuma yi suka kan tanadin dokar wani na daban, wanda ya ba da dama ga mutum ya kai karar masu zubar da ciki, tare da duk wani da yake da hannu ko taimaka wa a zubar.

Mista Biden ya ce wannan abu ya saba matuka, kamar yadda mai magana da yawun Fadar Amurkar, White House, Jen Psaki ke cewa:

” Dokar za ta hana mata damar samun kulawa ta fannin lafiya, musamman ma wadanda suke daga al’ummomin da ba ainahin fararen fata ba da kuma masu karamin karfi.”

Ta kara da cewa dokar ta kuma ba wa mutane wani ikon a kai karar duk wanda suke ganin ya taimaka wa wata mata wajen zubar da ciki, wanda zai iya hada wa da danginta, ko ma’aikatan lafiya, ko ma’aikatan ofis na asibiti ko ma wani bako da ba shi da wata alaka da matar da aka zubar wa da cikin, ko da kuwa tuka ta ya yi a mota ya kai ta.

Kuma duk mutumin da ya shigar da karar har ya yi nasara zai samu ladan dala dubu goma, abin da masu suka suke gani hakan zai zama wata dama neman cin garabasa da jama’a za su yi ta nema ido rufe.

Mai yaki da zubar da ciki Eva Alper ta nufi wasu mata a wajen wani asibiti da ake zubar da ciki a Texas

Wannan na daya daga cikin matakai na baya-bayan nan na takaita zubar da ciki a jihohin da ke karkashin ikon ‘yan jam’iyyar Republican.

Sun samu kwarin guiwa ne daga rinjayen da masu ra’ayin rikau ke da shi a cikin alkalan kotun kolin Amurkar, kotun da za ta iya dakatar da dokar ta Texas, amma kuma ta ki amsa bukatar da aka shigar gabanta ta gaggawa ta daukaka kara wadda da za ta hana dokar fara aiki.

Masu kare hakkin mata na fargabar cewa muddin aka bar wannan doka ta dore za ta bude kofa tare da karfafa guiwar samar da wasu dokokin makamantanta da kuma karfin halin kalubalantar ‘yancin zubar da ciki da ake da shi a Amurka.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings