X

Ƴan bindiga sun kashe ɗan sanda a Anambra

Wasu yan bindiga a Jiya Lahadi sun kashe wani ɗan sanda a wani shingen bincike a Jihar Anambra.

Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya reshen Anambra Tochukwu Ikenga yana tabbatar da lamarin.

Ya bayyana cewa jami’an ƴan sandan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan wanda a sanadin haka ne dan sanda ɗaya ya rasu.

Haka kuma wasu rahotanni na cewa yan bindigar sun kai hari a gidan watsa labarai na Jihar Anambra reshen Onitsha.

Rahotanni sun ce ƴan bindigan har sun ƙona motar gidan watsa labaran da ke ajiye da kuma wata mota ta ma’aikacin wurin da ya yi aikin dare.

Categories: Labarai
twinsem2:
X

Headline

You can control the ways in which we improve and personalize your experience. Please choose whether you wish to allow the following:

Privacy Settings