Bai wa Pantami matsayin farfesa haramtacce ne – ASUU
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU ta nemi a soke matsayin farfesa da aka bai wa ministan sadarwa na ƙasar Isa Ali Pantami.
ASUU ta bayyana wannan matsayar ne a ƙarshen taron sugabanninta da aka gudanar ranar Litinin, inda tace ɗaga darajar Pantami zuwa matsayin Farfesa haramtacce ne.
Shugaban ƙungiyar Farfesa Emmanuel Osodoke yayin wani taron manema labarai yace “ba yadda za a yi kana minista kuma kana karantarwa a lokaci guda.”
Ƙungiyar ta ce dole ne Pantami ya yi murabus daga matsayin minista sannan a gurfanar da shi saboda yin aiki biyu a ƙarƙashin gwamnati guda.
To sai dai har lokacin rubuta wannan labari Sheikh Isa Ali Pantami bai ce komai ba kan wannan zargi.
A lokacin da jami’ar ta Owerri ta ɗaga darajar Pantami zuwa Farfesa a ɓangaren tsaron intanet ta ce ya bi dukkan matakan da malaman jami’a ke bi kafin su samu matsayin mafi kololuwa a jami’a.
A wata sanarwa a lokacin tace buƙatar da Pantami ya miƙa ta tsallake matakai shida kafin majalisar zartarwar jami’ar ta amince da ita.
To amma tun a lokacin, ƙungiyar ta malaman jami’a, ASUU ta yi watsi da bai wa Pantami mastayin na Farfesa.
Ko baya ga uwar ƙuniyar ta ASUU, ita ma ƙungiyar ta malaman jami’o’in ta Abubakar Tafawa Balewa Bauchi inda a nan ne Dakta Pantami ya shafe lokaci mai tsawo yana koyarwa ta nesanta kanta daga tura saƙon taya murna kan ɗaga darajar Pantami zuwa matsayin Farfesa.
Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa jami’ar ta Tafawa Balewa ta taya Pantami murna, sai dai nan take resehen ƙungiyar ASUU na jami’ar ya ce bai gamsu cewa an bi duka matakan da suka kamata ba wajen amincewa da matsayin na Farfesa.
To sai dai tun a watan Satumbar na bara, ƙungiyar de ke fafutukar kare muradun Musulmai ta Najeriya MURIC ta ce ƙabilanci ne da nuna bambamcin addini ya sa ake ɗaga jijiyar wuya kan batun bai wa Pantami matsayin Farfesa.
Ba kan Pantami farau ba
MURIC tace rashin aikin yi ne da kuma ragwanta za su sa a ringa ta da jijiyar wuya kan batun.
Ƙungiyar mai rajin kare Musulmai ta Najeriya ta ce mutane da dama sun samu matsayin farfesa a lokacin da suke aikin gwamnati.
MURIC ta ce a shekarar 2013 ministan lafiya na Najeriya Dokta Muhammad Ali Pate ya samu matsayin Farfesa daga wata jami’ar Amurka a lokacin da yake aikin minista.
Ta ce akwai kuma kwamishina a jihar Edo da ta samu matsayin Farfesa a jami’ar Legas, haka kuma akwai wani kwamishinan gwamnatin Legas da shi ma ya samu farfesa a lokacin da yake kwamishina, har ma da ƙarin wasu da dama da suka samu ƙarin matsayin farfesa.
Ko ASUU na da hurumin kan ba da matsayin farfesa?
Farfesa a tsangayar shari’a na jami’ar Bayero Farfesa Mamman Lawan Yusufari, inda yace a doka ƙungiyar ASUU ba ta da hurumi kan bai wa mutum matsayin farfesa.
A cewarsa, hukumar gudanarwar jami’a ce ke da alhakin amincewa da cewa wani malami ya cancanci zama farfesa bayan sun gamsu da cika duk sharuɗan da aka gindaya kafin mutum ya kai matsayin.