Shugaban Sashen Ƙididdiga na Najeriya, Dr Simon Harry, ya ce ƙarancin man fetur da ake fama da shi a wasu sassan ƙasar zai iya shafar hauhawar farashi a watan Fabarairu idan ba a ɗauki mataki ba.
Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a jiya Talata, Dr Harry ya ce ƙarancin man zai haifar da fargaba kan tattalin arziki ta yadda farashin kayan abinci za su tashi da kuma ladan ayyuka.
“Ko muna so ko ba ma so, masu safarar kaya za su yi amfani da wannan damar wajen ƙara kuɗin dako,” in ji shi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce an samu raguwa a hauhawar farashin kaya a Najeriya a watan Janairun da ya gabata da kashi 0.34 cikin 100 idan aka kwatanta da Disamban 2021.
Yanzu haka dai ana sayar da lita ɗaya ta man fetur ɗin kan N500 ko fiye a Abuja babban birnin ƙasar, yayin da gidajen mai ƙalilan ne ke sayar da man.
A gefe guda kuma, kamfanin mai na Najeriya, NNPC, ya ce ya bayar da umarnin dakon mai daga manyan rumbuna da kuma sayar da shi a gidajen mai a fadin kasar, ba dare ba rana a kokarin kawo karshen matsalar.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jiya Talata, NNPC ya ce yana ba wa ‘yan kasar tabbacin daukar matakan da suka dace domin hanzarta samar da man a fadin kasar.